Isa ga babban shafi
Afirka

Kagame ya bukaci gaggauta amincewa da sauyin kungiyar AU

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya bukaci shugabannin kasashen Afirka da su gaggauta amincewa da bukatun kawo sauyi kan yadda ake tafiyar da kungiyar kasashen Afirka a wajen wani taro na musamman da aka gudanar yau a Addis Ababa.

Paul Kagame Shugaban Rwanda kuma Shugaba kungiyar Afirka ta AU
Paul Kagame Shugaban Rwanda kuma Shugaba kungiyar Afirka ta AU Madoka Ikegami/POOL Via REUTERS
Talla

Kagame yace lokaci yayi da za’a sake fasalin kungiyar ta zama mai dogaro da kanta, maimakon wadda ta dogara ga taimako daga kasashen duniya da kuma bata karfin fada aji kan duk wasu matsalolin da suka shafi nahiyar.

Shugaban Rwanda dake kamala wa’adin sa na shugabancin kungiyar a watan Janairu mai zuwa yace a karon farko kungiyar ta samu nasarar kaddamar da asusun zaman lafiya da zai dinga kai dauki mai kunshe da Dala miliyan 400.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewar wasu kasashen Afirka na dari dari da shirin kungiyar na katsalandan domin sasanta rikicin da ake samu a cikin mambobin kungiyar, abinda basa sa goyan bayan shirin na shugaba Kagame.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.