Isa ga babban shafi
Nijar-Mali

'Yan ta'adda sun hallaka jami'an tsaron Nijar 2 a wani farmaki

Wasu Yan bindiga da ake zargin Yan ta’adda ne daga kasar Mali, sun kai hari Makalondi da ke kan iyakar Nijar da Burkina Faso inda suka kashe jami’an tsaro guda biyu, kana suka jikkata wani guda.

Makamantan hare-haren kan jami'an tsaron na Nijar tare da hallaka wasu daga ciki ba sabon abu ba ne, sai dai a wannan karon shigarsu sansanin wanda ke cike da matakan tsaro ana ganin babbar barazana ce ga kasar ta Nijar.
Makamantan hare-haren kan jami'an tsaron na Nijar tare da hallaka wasu daga ciki ba sabon abu ba ne, sai dai a wannan karon shigarsu sansanin wanda ke cike da matakan tsaro ana ganin babbar barazana ce ga kasar ta Nijar. 路透社
Talla

Rahotanni sun ce Yan bindigar da ke haye akan Babura dauke da makamai, sun kai harin ne sansanin jami’an tsaron, inda suka kwashe mintina 15 suna musayar wuta.

Bayanai sun ce daga bisani an kai Karin jami’an tsaro inda aka kai harin da ke da nisar akalla kilomita 100 daga birnin Yammai.

Makamantan hare-haren kan jami'an tsaron na Nijar tare da hallaka wasu daga ciki ba sabon abu ba ne, sai dai a wannan karon ana ganin shigarsu sansanin wanda ke cike da matakan tsaro babbar barazana ce ga tsaron kasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.