rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar CPJ ta karrama Ahmed Abba na RFI Hausa

media
Ahmed Abba da Cecile Megie Shugabar Rediyo Faransa Internationale RFI a Amurka rfi hausa

Kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya CPJ ta karrama Ahmed Abba wakilin sashen hausa na Radio France Internationale daga Kamaru a matsayin wanda ya lashe kyauta ta shekarar 2017 a New York dake kasar Amurka.


Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta CPJ mai ofishi a birnin New York na Amurka ta ce, Ahmed Abba ‘dan jarida da ya lashe kyautar ya fuskanci wulakanci daga bangaren gwamnati Kamaru da barazanar kisa da kuma dauri .

Wakilin sashen hausa na Radio France International Ahmed Abba da gwamnatin Kamaru ta kama a shekarar 2015 bisa zargin alakarsa da kungiyar Boko Haram, an yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari duk da cewa, ya musanta zargin .

Ahmed Abba ya samu rakiyar Cecile Megie Shugabar Rediyo Faransa Internationle RFI zuwa New York na kasar Amurka.

Daraktan kungiyar Joel Smith ya ce ana bada irin wannan kyauta ne ga ‘yan jaridun da suka fuskanci barazanar kisa ko dauri.