Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Majalisar Dattijan Najeriya ta yi makokin soji 70 da Boko haram ta kashe

Majalisar Dattijan Najeriya ta dage zamanta na yau Alhamis don martabawa ga dakarun sojin kasar fiye da 70 da suka rasa rayukansu a wani harin boko Haram kan sansaninsu da ke garin Maiduguri na jihar Borno ranar Litinin.

Majalisar ta amince da kafa kwamiti na musamman don bibiyar yadda za ta fara taimakawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a yaki da Boko Haram.
Majalisar ta amince da kafa kwamiti na musamman don bibiyar yadda za ta fara taimakawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a yaki da Boko Haram. REUTERS/Afolabi Sotunde)
Talla

Shugaban masu rinjaye Majalisar Bala Na’Allah a jawaban da ya gabatar na neman dage zaman na yau, ya ce kwamandan tawagar da boko Haram ta farmaka dan kawunsa ne Leutenal Sakaba, da ya sadaukar da rayukarsa shi da sauran sojojin wajen bayar da tsaro ga Najeriyar.

Jaridar Premium times da ake wallafawa a Najeriyar ta ruwaito cewa  Boko Haram ta farmaki bataliya ta 157 ta sojin Najeriyar da ke Matete a karamar hukumar Abadan ta jihar Borno tare da hallaka soji fiye da 70 baya ga kwashe tarin makamai, batun da kawo yanzu ma’aikatar tsaron kasar da Rundunar soji ta gaza cewa uffan.

A jawabinta shugabar marasa rinjaye Biodum Olujimi ta diga ayar tambaya kan gwamnatin Najeriya game da yadda tarin sojoji ke ci gaba da rasa rayukansu a yaki da boko haram tsawon lokaci.

Shi kuwa mataimakin shugaban Majalisar Ike Ekweremadu cikin jawabansa ya nuna damuwa kan yadda hare-haren na Boko Haram ke ci gaba da lakume rayukan sojin kasar da ma na fararen hula, yyainda ya bukaci gwamnati ta sauya salon yaki da ayyukan ta’addancin kungiyar ta Boko Haram.

Ka zalika Sanata Ekeremadu ya nemi samar da mafita ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a fagen daga, la’akari da yadda ‘ya’yansu da matansu kan shiga halin tsaka mai wuya bayan mutuwar Iyayensu.

Tuni dai majalisar ta amince da kafa wani kwamiti na musamman don kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan sojin da suka rasa rayukansu tare da lalubo hanyoyin da za a rika taimakawa iyalan mamatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.