rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harin Tumour ya jefa jama’a cikin fargaba

media
Wani yankin yan gudun hijira a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar irinnews.org

Hankulan jama’a sun tashi a yankin Diffa da ke gabashin Jamhuriyar Nijar, bayan da wasu ‘yan bindiga da ake zaton cewa magoya bayan Boko Haram ne suka kashe mutane 8 da ke aiki da wani kamfanin haka riyoji mai suna Foraco a garin Toumour.


Bayanai sun ce mutanen na gina rijiya ne domin jama’ar da ke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira a garin Toumour, lamarin da a cewar kungiyoyin fararen hula a Diffa ba karamar matsala zai haifar wa makomar jama’a ba.

Harin da yan bindigan suka kai jiya da asuba a garin na Tumour ya wakana ne a dai dai lokacin da jami’an tsraro dake kula da kare lafiyar ma’aikantan kamfanin Foraco suka janye daga fadar magajin garin Tumour wurin da aka sauke ma’aikantan kamfanin Foraco.