Isa ga babban shafi
Nijar-Boko Haram

Boko Haram ta sace 'yammata 15 a Nijar

Rahotani daga Jamhuriyar Nijar na cewa wasu mayakan boko haram sun sake kai hari garin Toumour da ke jihar Diffa a yammacin jiya tare da sace 'yammata akalla 15.

Wannan dai ne karo na biyu cikin mako guda da Boko Haram ke kai kazamin hari garin na Toumour da ke jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar.
Wannan dai ne karo na biyu cikin mako guda da Boko Haram ke kai kazamin hari garin na Toumour da ke jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar. RFI/OR
Talla

Wata majiya daga garin na Toumour da ta tabbatar da afkuwar lamarin ta ce ayarin mayakan su kusan 50 ne dauke da muggan makamai suka kaddamar da harin tare da yin awon gaba da 'yammatan.

Kawo yanzu dai babu wani rahoto da ke nuna cewa sun kashe mutane kafin tafiya da 'yammatan 15.

Makamantan hare-haren na Boko Haram na ci gaba da tsananta a garin na Toumour inda ko a ranar alhamis din da ta gabata sai da mayakan na Boko Haram suka hallaka ma’aikatan wani kamfanin samar da ruwan sha na Foraco guda 8 da ke kan aiki a garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.