rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Tarayyar Afrika Benin

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa zata mayarwa Benin da kayakin tarihi 26

media
kayakin tarihi daga wasu kasashen Afrika Siegfried Forster / RFI

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a jiya juma’a ya amincewa don gani an mayarwa Jamhuriyar Benin wasu kayakin tarihi 26 da turawan mulkin mallaka suka yi awon gaba da su a lokacin mulkin mallaka.


Daukar wannan mataki na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kwamitin dake da nauyi gudanar da bincike dangane da tasirin mayarwa kasashen Afrika kayakin tarihin ya mika zuwa fadar Shugaban kasar sakamakon bincike da ya gudanar a kai.

Fadar Shugaban kasar Faransa ta bukaci sauren kasashen Turai suyi koyi da Faransa wajen mayar da irin wadanan kayakin tarihi zuwa kasashen su na asali.