Isa ga babban shafi
Uganda

Mutane da dama ne suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a Uganda

A Uganda wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife a tafkin Victoria, yayinda da mutanen da suka mutu ya kai 22.Ana zaton kwale kwalen na dauke da fiye da fasinjoji da ya saba dauka ne, adadin da ya ninka iya mutanen da ya kamata ya diba, lamarin da ya sa ya kife a cewar wasu daga cikin mutanen da suka cira daga hatsarin

Masu aikin ceto  bayan wani hatsarin jirgin ruwa sama tafkin Victoria tsakanin Uganda da Tanzania da Kenya
Masu aikin ceto bayan wani hatsarin jirgin ruwa sama tafkin Victoria tsakanin Uganda da Tanzania da Kenya Reuters TV/via REUTERS
Talla

Kimanin mutane 22 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da aka ceto 40 daga cikin fasinjoji da ke cikin jirgin.

Tuni al’ummar yankin suka shiga aikin taimako tare da jami’an bada agajin gaggawa don ceto wadanda hatsarin ya auku saman su.

Gwamnatin Uganda ya zuwa yanzu ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ba ta yi karin haske ba kan adadin mutanen da ke cikin kwale-kwalen.

Ko a watan Satumba na shekarar bana, sai da sama da mutane 200 suka rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da ke dauke da su ya yi hatsari a Tanzania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.