Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Tsohon hafsan sojin Burkina Faso ya musanta jagorantar juyin mulki

Tsohon hafsan sojin Burkina Faso da ya jagoranci juyin mulkin shekarar 2015 Janar Gilbert Diendere ya gurfana a gaban kotu, inda ya musanta cewar ba shi ya jagoranci kifar da gwamnatin kasar ba.

Tsohon hafsan sojin Burkina Faso da ya jagoranci juyin mulkin shekarar 2015 Janar Gilbert Diendere. 23/09/2015.
Tsohon hafsan sojin Burkina Faso da ya jagoranci juyin mulkin shekarar 2015 Janar Gilbert Diendere. 23/09/2015. Reuters
Talla

Yayin gabatar da bayanin sa a gaban kotun sojin kasar, Janar Diendere, yace ba shi ya kitsa ko ya bada umurni ko ya kuma shirya juyin mulkin da aka yi ranar 16 ga watan Satumbar shekarar 2015.

Diendere ne shugaban zaratan sojin dake gadin fadar shugaba Blaise Compaore wanda ya kwashe shekaru 27 yana mulkin kasar.

Ya kuma rike mukamin shugaban kasa na wani lokaci bayan an kori Compaore daga karagar mulki, abinda ya haifar da tashin hankalin da ya kasha mutane 14 da raunata 270.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.