Isa ga babban shafi
Kamaru

Bankin BAD ya amincewa baiwa Kamru Bashi domin gina Hanyoyi

Bankin Raya kasashen Afirka BAD ya sanar da amincewasa kan bashin euro miliyan 18 domin gina hanya mota a Kamaru wanda zata tashi daga Arewa zuwa Yammacin kasar.

sabuwar hanyar da aka gina
sabuwar hanyar da aka gina © RFI/Sayouba Traoré
Talla

Bankin ya ce aikin gina hanyar wadda ta shiga cikin tsarin ayyuka na 3 na tallafawa harkokin sufurin Kamaru, zai taimaka wajen safarar kayayaki da mutane daga sassan kasar.

Bankin ya kuma ce aikin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kuma kasuwanci tsakanin al’ummar kasar.

Wannan aikin da zai ci kilomita 365 shine irin san a 3 da Bankin ke gudanarwa a kasar a karkahsin shirin sa na musamman na inganta rayuwar jama’a, musamman wadanda ke iyakar Najeriya.

Bankin yace Arewa maso yammacin kamaru na da kayayakin bunkasa tatatlin arziki da suak hada da albarkatun noma da kiwo da kamun kifi da yawon bude ido da wuraren shakatawa da dama.

Bankin yace za’a fara aikin a watan Disamba mai zuwa yayin da ake saran kamala shi a shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.