rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sama da yara miliyan daya na bukatar agaji a Jamhuriyar Afrika

media
Biyu bisa Uku na yara kanana a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na bukatar agajin gaggawa na magani da abinci. unicef.org

Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya UNCIEF, yace kimanin kashi biyu bisa uku, na kananan yaran dake jamhuriyar Afrika ta tsakiya, na bukatar agajin gaggawa.


Asusun na UNICEF ya bayyana hakan ne cikin wani rahotonsa da yace, yawan yaran da ke tsananin bukatar tallafin ya kai miliyan daya da rabi, kuma akalla dubu 43,000 daga cikinsu na cikin hadarin rasa rayukansu a shekara mai kamawa, saboda rashin samun abinci.

Rahoton ya kara da cewa, Jamhuriyar Afrika ta tsakiya kasa ta biyu a duniya wajen fuskantar yawaitar mutuwar jarirai da mata masu juna biyu.

Tun a shekarar 2013 kasar ke fama da tashin hankali, biyo bayan yakin basasar da ya barke tsakanin mayakan sa kai na Seleka da suka hambarar da gwamnatin Francois Boazize da kuma mayakan Anti Balaka dake yakarsu.