rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harin nakiya ya hallaka mutane 5 a Burkina Faso

media
Wasu jami'an tsaron kasar Burkina Faso. AFP

Mutane biyar, hudu daga cikinsu jami’an ‘yan sanda sun hallaka a Burkina Faso, lokacin da motarsu ta taka wata nakiya da aka binne.


Harin ya auku ne a garin Boungou dake gabashin kasar, inda a baya bayan nan ake fuskantar karuwar hare-hare daga kungiyoyi masu da’awar jihadi.

Tawagar jami’an tsaron na kan aikin rakiyar wasu ma’aikatan hakar ma’adanai ne a lokacin da suka gamu da ajalin nasu.

Ko a watan Agutan da ya gabata akalla mutane 6 ne suka hallaka a makamancin harin na jiya, wanda ya kawo yawan jami’an tsaron Burkina Faso da suka hallaka a hare-haren zuwa 40, daga watan Augutan zuwa yanzu.