rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Senegal Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kaddamar da Macky Sall a matsayin dan takarar jam'iyya mai mulki

media
Bikin kaddamar da Macky a matsayin dan takara a zaben kasar SEYLLOU / AFP

Shugaba Macky Sall na Senegal yayi alkawari samar wa kasar daukaka matukar dai ya yi nasara a zaben da za a gudanar a ranar 24 ga watan fabarairun shekara mai zuwa, zaben da bangaren shari’a ya hana manyan masu adawa da shi damar tsayawa takara.


Macky Sall ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi jim kadan bayan da kawance jam’iyyun da ke mara masa baya a zaben mai zuwa ya kaddamar da shi a matsayin dan takara a wannan zabe domin sake shugabantar kasar karo na biyu.