rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Spain ta karbi wasu bakin haure

media
Wasu bakin haure da aka ceto daga cikin jirgin ruwan Aquarius REUTERS/Darrin Zammit Lupi

Gwamantin Malta ta karbi bakin haure 11 da suka share tsawon kwanaki 10 suna gararamba a kan tekun Mediterranean.

Wata kungiyar kasar Spain ce mai suna Proactiva Open Arms ce ta gabatarwa mahukuntan kasar ta Malta da wannan bukata, domin karbar bakin wadanda suka taso daga gabar ruwan kasar Libya.


Bakin haure da suka hada da yan Nijar,yan Somaliya, Sudan, Masar da Sanegal da jirgin ruwa mai suna Nuestra Madre Loreto ya ceto su a gabar ruwan kasar Lybia.

An dai bayyana cewa daya daga cikin bakin na fama da zazzabi da kuma aka garzaya da shi zuwa wani asibitin Malta.

Kasar Spain ta kasance kasa ta farko dake a matsayin kofa ga bakin haure kan hanyar su ta zuwa Turai duk da mantsin lamba da ta dau don dakile kwarrar bakin haure.