rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afrika ta kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

kasar Afrika ta kudu ta sanar da ficewa daga cikin matsalar tattalin ariziki

media
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa a taron gungun tattalin arziki na kasashen BRICS, a 26 yulin 2018 a Johannesburg. Themba Hadebe / POOL / AFP

A hukumance kasar Afrika ta kudu ta sanar da ficewa daga matsalar koma bayan tattalin arziki, bayan da ta samu habbakar kashi 2,2% a watanin ukun da suka gabata, kamar yadda cibiyar kididiga ta (StatsSA) ana yan watanni a gudanar da zaben yan majalisar dokoki kasar a wannan shekara ta 2019.


Kudaden shigar kasar, da ke kan gaba a jerin kasashe masu karfin tattalin arizikin masana’antu a nahiyar Afrika, sun hadu da nakasu har sau biyu, a wannan shekara ta 2018, da 2,6% a da kuma 0,7%, a watanin shidan farko na 2018, sakamakon zazzabin da tattalin arizikin kasar ya yi fama da shi.

A cewar cibiyar auna karfin tattalin ariziki ta kasar ta StatsSA, ci gaban tattalin arzikin da kasar ta samu ya faru ne sakamakon ingantuwar masana’antu, noma da kuma sufuri da aka samu a kasar ne.

Masani tattalin ariziki a kasuwar hada hadar kudaden waje ta Afrika ta kudu (FXTM foreign exchange) Lukman Otunuga, Ya ce kamata ya yi gwamnati ta kara karfafa guiwar ci gaban tattalin arizikin da aka samu, wajen da kara janyo masu zuba jari na kasashen ketare a kasar

Yanzu haka dai, darajar takardun kudin afrika ta kudu sun kara farfadowa, sakamakon fahimar junan da aka samu na baya bayan da ya kawo karshen yakin kasuwanci da aka buda tsakanin Amruka da China

Shekaru da dama da suka gabata Afrika ta kudu ke ta kokarin ganin ta fice daga matsalar koma bayan tattalin arizikin da ta samu kanta a ciki, da kuma rage gibin guraben ayukan yi da aka kiyasta cewa kimanin 27% na al’ummar kasar basu da ayukan yi.

A 2017 kasar ta samu ci gaban tattalin ariziki da kimanin 1,3% sai kuma (+0,6% 2016), a yayin da masharhanta tattalin arziki suka yi sashen cewa kasar zata samun ci gaban tattalin arrizikin da ya kai 1,8% a wannan shekara ta 2018.