rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Akwai jahilai fiye da miliyan 60 a Najeriya

media
Kashi 60 cikin 100 na adadin jahilan da Najeriya ke da su mata ne, galibi kuma kananan yara. AFP/BOUREIMA HAMA

Ma’aikatar ilimi a Najeriya ta yi ikirarin cewa kasar na da tarin jahilai akalla miliyan 60 da suka kunshi matasa maza da mata da kuma wadanda shekarunsu ke da yawa.


A jawabin da ya gabatar yayin taron ranar yaki da jahilci ta duniya, ministan ilimi na Najeriyar Malam Adamu Adamu ya ce akwai akalla yara miliyan 11 da basa zuwa makaranta a kasar.

Malam Adamu Adamu wanda ya samu wakilcin Mr Prinzo James mataimakin daraktan sashen kula da ilimin Firamare da Sakandire na Najeriyar, ya ce daga cikin adadin jahilan da suka gano kashi 60 cikin dari mata ne matasa.

A jawaban na sa, Adamu Adamu ya ce an samu raguwar jahilan da kasar ke da su bayan samar da makarantun yaki da jahilci da ya tilastawa dattijai da dama komawa karatu yayinda ya bukaci daukar mataki don kawar da jahilci a Najeriyar.

Malam Adamu Adamu ya ce akwai bukatar daukar kwararan matakai don kawar da matsalar jahilci a tsakanin al’ummar kasar nan da shekarar 2030, dalili kenan da ya sanya Gwamnatin kasar fara shirye-shiryen gabatar da wani shirin yaki da zalunci a ilahirin sassan kasar.