rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Burutai ya sake sauya kwamandan Operation lafiya dole

media
Sabbin sauye sauyen dai sun shafi kwamandodi da dama a matakai daban daban. AFP PHOTO/STRINGER

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da gagarumar garambawul ga kwamandodin rundunoninta da ke yaki da kungiyar boko haram a sassan kasar.


Daraktan yada labaran rundunar, Janar Sani Usman Kuka sheka, ya bayyana cewar an nada Manjo Janar OT Akinjobi a matsayin kwamandan runduna ta 3 da ke yaki da kungiyar boko haram, yayin da aka nada Manjo Janar MG Ali a matsayin kwamandan runduna ta 9, sai kuma Birgediya Janar BR Sinjen ya zama kwamanda runduna ta musamman da ke kai dauki.

Janar kuka sheka ya ce sauye sauyen sun shafi kwamandodi da dama a matakai daban daban.

A farkon makon nan ne Ministan tsaro Janar Mansur Dan Ali ya umurci shugaban rundunar sojin, Janar Tukur Buratai da ya koma Maiduguri da kuma aiwatar da sauye sauyen jami’an sojin domin sake fasalin yakin da suke da kungiyar boko haram.