Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Mannir Bature mataimakin shugaban kungiyar likitoci a Zamfara kan bayanan da ke nuna mata masu ciki 30 na mutuwa kowacce rana

Wallafawa ranar:

Kungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Zamfara ta ce akalla mata masu juna biyu 30 ne ke mutuwa a kowace rana cikin jihar, a dalilin matsaloli da suke fuskanta na lafiya.Mataimakin shugaban kungiyar likitocin jihar Dr Mannir Bature ne ya bayyana haka yayin ganawarsu da ‘yan takarar da ke neman kujerar gwamnatin jihar ta Zamfara. Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Mannir Bature mataimakin shugaban kungiyar likitocin ta jihar Zamfara kan kalubalen dake fuskantarsu da kuma mafita.

A jawaban da ya gabatar gaban 'yan takarar gwamna na jihar ta Zamfara, Dr Mannir Bature ya ce kowacce rana ana samun mutuwar kusan mata 30 lokacin haihuwa a jihar sakamakon rashin isassun kayan aikin kula da lafiyarsu.
A jawaban da ya gabatar gaban 'yan takarar gwamna na jihar ta Zamfara, Dr Mannir Bature ya ce kowacce rana ana samun mutuwar kusan mata 30 lokacin haihuwa a jihar sakamakon rashin isassun kayan aikin kula da lafiyarsu. Reuters
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.