rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ebola WHO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sudan ta Kudu za ta baiwa jami'an lafiyarta rigakafin Ebola

media
Wasu ma'aikatan lafiya yayin tsaftace akwatin gawar wani mutum da ya mutu a dalilin cutar Ebola dake garin Beni a Jamhuriyar Congo. 13/8/2018. Photo: John Wessels/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, tace hukumomin Sudan ta kudu za su yiwa jami’an kula da lafiyar su allurar rigakafin cutar Ebola saboda mu’amalar da suke yi kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Congo.


Ma’aikatar lafiyar kasar tace rigakafin da za ta yi tare da hukumar lafiyar, zai mayar da hankali kan jami’an ta dake aiki a Juba, Yei, Yambio da kuma Nimule.

Kasar Sudan ta kudu na daga cikin kasashen dake iyaka da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo inda cutar ta hallaka mutane 271 ya zuwa yanzu.

A ranar 19 ga watan Disamba za’a soma aikin yiwa ma’aikatan lafiyar na Sudan ta Kudun rigakafi, kuma tuni aka ware maganin rigakafin na Ebola 2,160.