rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Wasanni Gasar Cin Kofin Afrika Kwallon Kafa CAF Morocco

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Morocco ta musanta neman karbar bakuncin gasar AFCON

media
Ministan wasannin kasar Morocco Rachid Talbi Alami. Getty Images

Ministan wasannin Morocco, Rachid Talbi Alami, ya ce kasarsa ba ta cikin kasashen dake neman hukumar CAF ta basu damar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afrika AFCON ta 2019.


Ministan ya bayyana haka ne yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

A watan da ya gabata ne hukumar kula da kwallon Afrika CAF, ta kwace damar karbar bakuncin gasar ta AFCON daga hannun Kamaru, bisa dallilai na rashin kammala manyan ayyuka da kuma matsalolin tsaro.

Kafin kalaman ministan wasannin na Morooco rahotanni sun sha bayyana kasarsa da kuma Afrika ta Kudu, a matsayin kasashen dake kan gaba wajen zawarci ba su damar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar ta Afrika.

Gasar ta AFCON mai zuwa a watannin Yuni da Yuli a 2019, ita ce ta farko da kasashe 24 za su fafata a cikinta, maimakon kasashe 16 da suka saba halartar gasar.