Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotu ta daure mutane 2 rai da rai saboda cin naman mutum

Wata kotu a Afirka ta Kudu ta yankewa wasu mutane biyu Nino Mbatha da Lungisani Magubane hukuncin daurin rai da rai saboda samun su da laifukan kisan kai ta mummunar hanya da kuma cin naman mutane.

Lungisani Magubane daga bangaren hagu tare da Nino Mbatha wadanda kotu ta yankewa hukuncin daurin rai da rai, saboda samunsu da laifin kisan gilla.
Lungisani Magubane daga bangaren hagu tare da Nino Mbatha wadanda kotu ta yankewa hukuncin daurin rai da rai, saboda samunsu da laifin kisan gilla. Reuters/Rogan Ward
Talla

Alkali kotun Peter Olsen ya daure mutanen biyu ne bayan daya daga cikin su wato Mbatha mai shekaru 33 ya kai kan sa ofishin ‘yan sanda tare da jakar dake dauke da hannu da kafar mutum, inda ya shaida musu cewar ya gaji da cin naman mutane.

Da farko dai ‘yan sandan sun ki amincewa da ikrarin sa har saida ya kai su wani gida mai dauke da gawawakin mutanen da ya yiwa kisan gilla.

Afrika ta Kudu dai ba ta da doka ta kai tsaye dake hukunta wadanda aka kama da laifin cin naman dan adam, sai dai a karkashin dokokin kasar laifi ne mai girma a samu wani/wata da laifin sassara jikin dan adam ko kuma ajiye wani bangare ko sassan jikin mutum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.