Isa ga babban shafi
Habasha

Rikicin kabilanci ya tilastawa 'yan Habasha tserewa zuwa Kenya

Akalla mutane 21 aka hallaka tare da jikkata wasu 61, bayan shafe kwanaki biyu ana gwabza fada tsakanin wasu ‘yan kabilar Oromo da Somali a kudancin kasar Habasha.

Sansanin 'yan gudun hijira na Somare dake kan iyakar Habasha da Kenya a gaf da garin Moyale. 27/3/2018.
Sansanin 'yan gudun hijira na Somare dake kan iyakar Habasha da Kenya a gaf da garin Moyale. 27/3/2018. REUTERS/Baz Ratner
Talla

Fadan wanda ya tilastawa daruruwan ‘yan kasar tserewa zuwa cikin Kenya, ya barke ne a ranar Alhamis wayewar garin Juma’a da ta gabata a garin Moyale dake iyaka da kasar ta Kenya, yankin ake takaddama kan mallakarsa tsakanin kabilun na Oromo da Somali.

An dai samu karuwar tashin hankali a kudancin Habasha tsakanin ‘yan kabilar Oromo da sauran kabilu tun bayan rantsar ta sabon Fira Ministan kasar Abiy Ahmad a watan Afrilu, dan kabilar ta Oromo na farko da ya taba rike mukamin.

Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta wallafa kan tashin hankalin na baya bayan nan, ya tabbatar da cewa an yi amfani da manyan makamai yayin fadan kabilancin, abinda ya sa majalisar yin gargadin cewa, akwai yiwuwar fadan ya ketara cikin kasar Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.