Isa ga babban shafi
Najeriya-Kasuwanci

Bankin Diamond da na Access sun sanar da matakin hadewa waje guda

Wasu Bankunan kasuwanci a Najeriya sun sanar da matakin hadewa waje guda nan da sabuwar shekara a wani mataki da suka bayyana da yunkurin karfafa harkokin kasuwanci a kasar.Bankunan da suka kunshi Diamond da Access sun amince da matakin bayan jerangiyar tattauna da ta kai ga cimma mabanbantan yarjejeniya tsakaninsu.

A cewar bankin Diamond sai a watanni ukun farko na sabuwar shekara ne shirin hadewar zai kankama.
A cewar bankin Diamond sai a watanni ukun farko na sabuwar shekara ne shirin hadewar zai kankama. Solacebase
Talla

A cewar shugaban banki Diamond Mr Uzoma Dozie yayin wani taron manema labarai da ya kira yau a Lagos, ya ce bankin ya zabi hadewa da Access bayan yarjejeniyar da ya cimma tsakaninsa da abokanan huldarsa da kuma tattaunawar fahimtar juna tsakaninsa da Access wadda ta kai ga daukar matakin kin korar ma’aikata ko da bayan kammala hadewar.

A cewar Mr Uzoma sai a watanni ukun farko na shekarar 2019 ne yarjejeniyar za ta kammala, inda dukkanin Bankunan na Diamond za su juye zuwa Access sai dai ya sha alwashin cewa babu ko sisin kwastoma daya da zai yi ciwon kai.

Haka zalika bankin ya ce matakin ba wai na nuna koma baya ge bankin na Diamond ba ne, face wani yunkuri na habaka harkokin bankin a Najeriya, inda ya ce hadewar zai mayar da bankin mafi karfi da kuma yawan kwastomomi a nahiyar Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.