rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Madagascar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsoffin shugabanni na karawa da juna a Madagascar

media
Andry Rajoelina da abokin hamayyarsa Marc Ravalomanana Mamyrael / AFP

Tsoffin shugabannin Madagascar biyu na fafatawa da juna da zummar lashe kujerar shugabancin kasar a zagaye na biyu zaben da ke gudana a ranar Laraba.


Kasar na fatan kammala zaben cikin lumana tun bayan rikicin siyasar da ta yi fama da shi bayan Marc Rasvalomanana ya sauka daga kujerar shugabancin kasar sakamkon matsain lambar da ya fuskanta daga masu zanga-zanga a karkashin jagorancin Andry Rajoelina wanda ya gaje shi a karagar mulki a shekarar 2009.

‘Yan takarar biyu da suka kada kuri’unsu a babban birnin Antananarivo, sun yi alkawarin mancewa da banbancin da ke tsakaninsu, yayin da kowannensu ke cewa, zai amince da sakamakon zaben bayan fitar da shi.

A zagayen farko na zaben, Ravalomanana ya samu kashi 35.35 daga cikin 100, yayin da Rajoelina ya samu kashi 39.23, abin da ke nuna cewa, dukkaninsu sun sha gaban shugaban kasar na baya-bayan nan, Hery Rajaonarimampianina da ya yi na uku a zagayen farko a cikin watan Nuwamba.

An girke jami’an sojoji a sassa daban-daban don tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar al’umma a tsibirin kasar ta Madagascar.