rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Madagascar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rajoelina ya zarta abokan takararsa a zaben Madagascar

media
Hotunan 'yan takarar zaben shugabancin Madagascar (daga hagu zuwa dama) Marc Ravalomanana, shugaba Hery Rajaonarimampianina da Andry Rajoelina. REUTERS/Mike Hutchings/Thomas Mukoya

Yayin da ake ci gaba da kidayar kuri’un zaben shugabancin kasar Madagascar da aka kada a ranar Laraba, sakamakon wuci gadi ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Andry Rajoelina ke kan gaba.


Bayan kirga kashi daya bisa uku na yawan kuri’un da aka kada, Rajoelina na da kusan kashi 55, yayin da abokin hamayyarsa shi ma tsohon shugaban kasar ta Madagascar, Marc Ravalomanana ke da kashi 45.

Tuni dai Ravalomanana ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben inda yayi ikirarin shi ne da nasara a zaben.

A shekarar 2002 Ravalomanana ya zama shugaban Madagascar, sai dai bayan shekaru 7 masu zanga-zanga a karkashin jagorancin Rajoelina suka tilasta masa yin murabus, wanda a lokacin sojoji suka nada shi shugabancin kasar har zuwa shekarar 2014, kafin daga bisani shugaba Hery Rajaonarimampianina ya karba, wanda shi ma ke neman zarcewa a shugabancin kasar.

A ranar 9 ga watan Janairu mai zuwa ake sa ran tattara sakamakon zaben na shugaban kasa, da kuma sanar da wanda ya yi nasara.