rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Madagascar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rajoelina ya kama hanyar lashe zaben Madagascar

media
Dan takarar shugabancin Madagascar, Andry Rajoelina, yayin kada kuri'a a birnin Antananarivo. AFP

Sakamakon kidayar kuri’un zaben shugaban kasa da aka tattara a Madagascar daga ranar Alhamis zuwa Asabar, 22 ga watan Disamba, na nuni da cewa, tsohon shugaban kasar Andry Rajoelina ya kama hanyar lashe zaben.


Bayan kidaya kuri’u miliyan uku da rabi daga cikin miliyan 5 da aka kada, hukumar zaben kasar ta ce Rajoelina ya lashe kashi 55 da rabi daga ciki, yayin da abokin hamayyarsa wanda shi ma tsohon shugaban kasar ne, Marc Ravalomanana ya ke da kashi 44 da kusan rabi.

A mako mai zuwa ake sa ran kammala tattara sakamakon zaben, wanda Ravalomanana yayi ikirarin cewa an tafka magudi cikinsa.

Sai dai tawagar jami’an sa ido ta kungiyar tarayyar turai EU kan zaben na Madagascar, ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa an tafka magudi da dan takara Ravalomanana ke zargi.

A shekarar 2002 Ravalomanana ya zama shugaban Madagascar, sai dai bayan shekaru 7 masu zanga-zanga a karkashin jagorancin Rajoelina suka tilasta masa yin murabus, wanda a lokacin sojoji suka nada shi shugabancin kasar har zuwa shekarar 2014, kafin daga bisani shugaba Hery Rajaonarimampianina ya karba, wanda shi ma ke neman zarcewa a shugabancin kasar.