Isa ga babban shafi
Chadi

'Za a gaggauta dakile yaduwar hare-haren Boko Haram Tafkin Chadi'

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa Idris Deby na Chadi, sun bayyana fargaba kan yadda hare-haren Boko Haram ke cigaba da fadada a cikin kasashe zagayen Tafkin Chadi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Chadi Idriss Déby, yayin ziyarar kwanaki biyu a babban birnin kasar N'djamena. 23/12/2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Chadi Idriss Déby, yayin ziyarar kwanaki biyu a babban birnin kasar N'djamena. 23/12/2018. Ludovic MARIN / AFP
Talla

Shugabannin sun bayyana haka ne yayin taron hadin gwiwar da suka yi bayan kammala ziyarar aikin da shugaban na Faransa ya kai a Chadi,, inda suka bayyana bukatar ganin an gaggauta samar da kudaden tallafawa rundunar dakarun hadin gwiwa da G5 Sahel da ta kunshi sojojin Nijar, Chadi, Mali, Burkina Faso da Mauritania.

Shugaba Macron ya kuma jaddada tabbatar da ganin cewa kungiyar tarayyar turai EU, ta cika alkawarinta na baiwa rundunar ta G5 Sahel tallafin euro miliyan 55 akan lokaci.

Har yanzu dai rundunar ta G5 Sahel da ta kunshi dakaru dubu 4, ba ta soma ayyukanta na yakar ta’addanci gadan gadan ba, saboda karancin kudaden gudanarwa.

A watan Fabarairu na farkon shekarar 2018, kimanin kasashe 50 suka yi alkawarin baiwa G5 Sahel tallafin euro miliyan 400 domin karfafa rundunar, sai dai bayan watanni 10, euro miliyan 100 kawai suka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.