Isa ga babban shafi
Sudan

MDD ta bukaci gudanar da bincike kan zanga-zangar Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Sudan ta gudanar da bincike kan yadda aka samu hasarar rayukan mutane da dama yayin zanga-zangar adawa da karin farashin biredi da ta juye zuwa ta kin jinin gwamnati.

Wasu jami'an tsaron Sudan, yayin kokarin tarwatsa masu zanga-zanga da ke neman shugaban kasar Omar al-Bashir ya yi murabus.
Wasu jami'an tsaron Sudan, yayin kokarin tarwatsa masu zanga-zanga da ke neman shugaban kasar Omar al-Bashir ya yi murabus. AFP
Talla

Kiran na sakataren Majalisar Antonio Guterres ya zo ne jim kadan, bayan da gwamnatin ta Sudan ta sanar da cewa bayan barkewar zanga-zangar a ranar 19 ga Disamban da muke ciki, mutane 19 sun hallaka, ciki har da jami’an tsaro 2, yayin da akalla wasu mutanen 219 suka jikkata.

A wannan Juma’ar dai sai da ‘yan sanda suka tarwatsa sabbin gungun masu zanga-zanga sassan birnin Khartoum, Omdurman, Atbara da kuma Madani, zalika ma’aikatar cikin gidan kasar ta sanar da kama wasu mutane 10 dauke da alburusai dubu daya.

Sai dai a nata bangaren daraktar Amnesty a gabashin Afrika, Sarah Jackson ta ce, abin damuwa ne yadda jami’an tsaron ke amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar da ba sa dauke da makamai.

Jackson ta bukaci gwamnatin kasar da ta kawo karshe amfani da karfin da ya wuce kima don kauce wa ci gaba da zubar da jini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.