Qatar ta baiwa Mali motocin yaki masu sulke 24
Rundunar sojin Mali, ta ce Qatar ta mika mata motocin yaki masu sulke guda 24, domin taimaka mata a yakin da take kokarin murkushi hare-haren ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Daya daga cikin kwamandojin sojin Qatar Janar al-Ghaffari, ya ce motocin sulken za su taimakawa sojin Mali yayin sintiri ko kai farmaki a yankunan da mayaka masu da’awar jihadi ke binne nakiyoyi ko bama-bamai.
Janar al-Gaffari ya kuma shaidawa manema labarai a birnin Bamako cewa, daga yanzu Qatar da Mali za su ci gaba da tafiyar da alaka mai karfi tsakaninsu ta fuskar sha’anin tsaro, horar da sojoji da kuma makamai.
Taimakon na Qatar ya zo a dai dai lokacin da Mali ke kokarin shawo kan hare-haren ta’addanci a wasu sassanta, kalubalen da ta ke fuskanta tun bayan korar mayakan ‘yan tawaye daga yankin arewacin kasar da suka taba mamayewa a shekarar 2012, wadanda har yanzu suke iko da wasu sassansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu