Isa ga babban shafi
Sudan

Masu zanga-zanga za su sake tunkarar fadar gwamnati a Khartoum

Gamayyar kungiyoyin fararen hula a Sudan, sun sake yin kira ga masu zanga-zanga su sake fita domin yin tattaki zuwa fadar gwamnati da ke Khartoum, da nufin tilastawa shugaban kasar Omar al-Bashir yin murabus.

Masu zanga-zanga a birnin Khartoum na Sudan, da ke neman shugaban kasar Omar al-Bashir ya yi murabus.
Masu zanga-zanga a birnin Khartoum na Sudan, da ke neman shugaban kasar Omar al-Bashir ya yi murabus. Reuters
Talla

Sanarwar da gamayyar kungiyoyin ta fitar, ta ce za'a soma tattakin za ranar Litinin.

Ranar 25 ga watan Disamba, kungiyoyin suka shirya makamanciyar zanga-zangar, amma ‘yan sanda suka watsa su, ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashi mai kisa.

Da fari dai daruruwan ‘yan kasar ta Sudan sun soma zanga-zanga kan karin farashin biredi a ranar 19 ga Disamba, daga bisani kuma ta juye zuwa neman saukar shugaba al-Bashir daga mulki.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce zuwa yanzu, jami’an tsaron Sudan sun kama ‘yan jaridu da dama, da jagororin ‘yan adawa. Sai dai ma’aikatar tsaron kasar ta musanta zargin.

Zuwa yanzu mutane 19 suka hallaka a jerin zanga-zangar da ke ci gaba da gudana a alkalumman gwamnati, yayin da kungiyar Amnesty International ta ce yawansu ya kai 37.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.