Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

An soma dakon sakamakon zaben Jamhuriyar Congo

‘Yan adawa a Jamhuriyar Congo, sun koka bisa yadda zaben shugabancin kasar ya gudana a ranar Lahadi, wanda suka ce an fuskanci matsaloli da kuma tafka kura-kurai, da suka hada da lalacewar injinan zabe, da kuma cin zarafin magoya bayansu.

Wasu ma'aikatan hukumar zaben Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo CENI, yayin soma kidayar kuri'u a birnin Kinshasa. 30/12/2018.
Wasu ma'aikatan hukumar zaben Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo CENI, yayin soma kidayar kuri'u a birnin Kinshasa. 30/12/2018. REUTERS/Baz Ratner
Talla

Korafin ‘yan adawar na zuwa ne a dai dai lokacin da al’ummar kasar da ma duniya ke dakon sakamakon zaben, wanda a karon farko zai bada damar sauyin mulki cikin ruwan sanyi, tun bayan samun ‘yancin kan kasar daga Belgium a shekarar 1960.

Rahotanni sun ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a mafi akasarin sassan kasar, sai dai an fuskanci tashin hankali a wasu yankunan.

Shaidun gani da ido sun ce, wani jami’in dan sanda ya harbe mutum guda a wata rumfar zabe da ke kudancin lardin Kivu a arewacin Jamhuriyar ta Congo, sakamakon takaddamar da ta barke tsakaninsu, hakan yasa shi ma dan sandan ya rasa ransa, bayan dukan kawo wukar da dandazon jama’ar da ke wajen suka yi masa.

A ranar 15 ga watan Janairu ake sa ran sanar cikakken sakamakon zaben shugaban kasar, sai kuma rantsar da wanda ya yi nasara a ranar 18 ga watan na Janairu.

Wasu dai na bayyana fargaba dangane da abin da ka iya biyo bayan zaben na Jamhuriyar Congo, la’akari da sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da cibiyar sa ido kan siyasar Jamhuriyar Congo ta gudanar mai hedikwata a New York.

Sakamakon kuri’ar ya nuna cewa, jagoran ‘yan adawa Martin Fayulu ke kan gaba wajen farin jini tsakanin 'yan takara da kashi 44 na yawan magoya, sai kuma Tshisekedi mai kashi 24, yayin da dan takarar shugaba Joseph Kabila, Emmanuel Ramazani Shadary, ke da kashi 18.

Zalika sakamakon kuri’ar ya ce, tsakanin kashi 43 zuwa 53 na ‘yan kasar sun ce ba za su amince da sakamakon zaben ba, muddin dan takarar shugaba Kabila ne yayi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.