Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Faransa ta nemi Congo ta mutunta 'yancin fadar albarkacin baki

Faransa ta bukacin gwamnatin Jamhuriyar Congo ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, biyo bayan matakinta na katse hanyar sadawar Intanet da kuma takaita aikin wasu ‘yan jarida da ke sa ido kan zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar Lahdi.

Kiran na Faransa na zuwa ne bayan hukumar zabe ta fitar da sanarwar cewa ba lallai a iya sanar da sakamakon zaben a ranar da aka alkawarta ba.
Kiran na Faransa na zuwa ne bayan hukumar zabe ta fitar da sanarwar cewa ba lallai a iya sanar da sakamakon zaben a ranar da aka alkawarta ba. REUTERS/Baz Ratner
Talla

Kiran dai na zuwa a dai dai lokacin da shugaban hukumar zaben Jamhuriyar ta Congon Corneille Nangaa, ya ce akawai yiwuwar dage lokacin bayyana sakamakon zaben daga ranar lahadi mai zuwa, zuwa wani lokaci daban.

Kawo yanzu dai dan takarar bangaren adawa da kuma dan takarar Jam'iyya mai mulki na ci gaba da ikirarin nasara a zaben kasar mai cike da hargitsi.

A bangare guda itama Majami’ar Katolika ta yi gargadin cewa ta na sane da wanda ya lashe zaben shugabancin kasar a don haka ka da gwamnatin ta yi yunkurin sauya sakamako.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.