Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Kasashe sun matsawa Kabila kan sakamakon zaben Congo

Manyan kasashe a ciki da wajen Nahiyar Afrika na ci gaba da matsawa shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila, kan tilas ya mutunta ra’ayin jama’a da suka kada kuri’a a zaben shugabancin kasar.

Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila. Kenny Katombe/Reuters
Talla

A wannan Lahadi 6 ga watan Janairu aka tsara sanar da sakamakon, sai dai, da yammacin Asabar, hukumar zaben kasar CENI, ta sanar da dagewa zuwa makon gobe, bisa dalilin har yanzu, kasa da rabin kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar aka samu tattarawa.

Matakin dai ya jefa al’ummar Jamhuriyar Congon cikin zaman dar-dar, bayan da a Alhamis din da ta gabata, majalisar shugabannin Cocin Katolika na kasar, mai wakilai akalla dubu 40 da ke sa ido kan zaben, ta ce ta san wanda yayi nasara tsakanin ‘yan takara 21 da suka fafafata.

Wata kuri’ar jin ra’ayi da wata cibiyar sa ido kan siyasar Jamhuriyar Congo ta gudanar mai hedikwata a New York, ta nuna cewa jagoran ‘yan adawa Martin Fayulu ke kan gaba wajen farin jini tsakanin 'yan takara da yawan magoya baya kashi 44, sai kuma Tshisekedi mai kashi 24, yayin da Shadary, dan takarar shugaba Joseph Kabila ke da kashi 18.

Zalika sakamakon kuri’ar ra’ayin ya nuna cewa, tsakanin kashi 43 zuwa 53 na ‘yan kasar sun ce ba za su amince da sakamakon zaben ba, muddin dan takarar shugaba Kabila ne yayi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.