Isa ga babban shafi
Sudan

Al'ummar Sudan na makokin wadanda suka mutu a zanga-zanga

Dubban Jama’a na ci gaba da wani gangami a sassan gabashin Sudan don nuna alhininsu kan mutanen da suka rasa rayukansu a zanga-zangar makwanni biyu da al’ummar kasar suka shafe suna yi don nuna bacin ransu da halin matsin rayuwar da su ke fuskanta.

Akalla mutane 800 hukumomin Sudan suka kame ciki har da shugabannin adawa bayan barkewar zanga-zangar.
Akalla mutane 800 hukumomin Sudan suka kame ciki har da shugabannin adawa bayan barkewar zanga-zangar. REUTERS
Talla

Zanga-zangar wadda ta barke tun ranar 19 ga watan Disamban bara bayan matakin karin farashin burodi da gwamnatin kasar ta dauka zuwa ninki 3 da asalin farashin da al’umma suka saba siya, ta yi sanadin mutuwar mutane 19 a cewar hukumomin kasar.

Sai dai kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce mutane 37 ne suka mutu ciki har da wadanda Jami’an tsaron kasar suka harbe har lahira kawai don sun hau manyan tituna suna nuna fushinsu.

A yankin Gadaref na gabashin kasar inda zanga-zangar ta faro akalla mutane 6 aka harbe har lahira, dubban jama’a sun cika tituna don nuna alhinin mutanen da suka mutu a zanga-zangar.

Tun bayan fara zanga-zangar akalla mutane 800 hukumomin Sudan suka kame tun bayan fara zanga-zangar wadda ta birkita siyasar kasar ciki har da shugabannin adawa.

Sai dai a jiya Litinin Ministan harkokin wajen kasar Ahmed Bilal Osman ya ce an shawo kan masu zanga-zangar inda gwamnati ke kokarin kwantar da hankulan talakawan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.