rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cote d'Ivoire

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsohon Shugaban Cote D'Ivoire bai kawar da yiyuwar tsayawa takara ba

media
Henri Konan Bédié tdohon Shugaban kasar Cote D'Ivoire SIA KAMBOU / AFP

Tsohon shugaban Cote d’Ivoire Henri Konan Bédié bai kawar da yiyuwar sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za a yi shekara ta 2020 ba, bayan da ya kawo karshen kawancen da ke tsakanin jam’iyyarsa da ta shugaba mai ci Alassane Ouattara ba.


A zantawarsa da wakilin rfi da kuma na kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce abu ne yiyuwa ya sake tsayawa takarar, tare da bayyana yiyuwar yin kawance da tsohon madugun ‘yan tawayen kasar Guillaume Soro a zaben na badi.

Shekaru biyu da suka gabata kenan da tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie ya sanar da kawo karshen kawance na jam’iyyar PDCI da jam’iyyar Shugaban kasar RDR, ganin sauyi da aka samu bayan da Shugaban kasar ya kaucewa matsayar da aka cimma a baya.