rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Emmerson Mnangagwa Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Farashin litar mai daya ya haura naira dubu a Zimbabwe

media
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa. REUTERS/Philimon Bulawayo

Shugaban Zimbabwe, Emmerson Manangagwa ya sanar da karin farashin litar man fetur da sauran albarkatunsa.


Manangagwa ya ce matakin ya zama tilas domin kawo karshen karancin man da kasar ke fuskanta, mafi muni da suka taba fuskanta cikin shekaru 10.

A lokacin da yake sanar da matakin a jiya Asabar, shugaban na Zimbabwe, ya ce farashin litar mai ya koma dala uku da doriya, kwatankwacin naira dubu 1 da 200, daga dala daya, wato dai dai da naira 350.

Matakin kara farashin albarkatun man da gwamnatin Zimbabwe ta dauka, ya zo ne bayan da ta sha alwashin samar da wani sabon kudin kasar cikin shekara daya, domin kawo karshen matsalar tattalin arzikin da take fuskanta.