Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Fulani sun gudanar da zanga-zanga a Burkina Faso

A Burkina Faso kungiyoyin Fulani da dama ne suka gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin kasar Ouagadougou a jiya asabar, biyo bayan kisan gila da aka yiwa wasu yan uwan su a garin Yirgou dake arewacin kasar a wani kazamin hari da wasu yan jihadi suka kai yankin.

Roch marc Christian Kaboré Shugaban Burkina Faso a garin Yirgou
Roch marc Christian Kaboré Shugaban Burkina Faso a garin Yirgou http://lefaso.net
Talla

Jajubirin sabuwar shekarar 2019 ne mahara dauke da mugan makamai suka afkawa garin na Yirgou tareda kashe mutane 49, yayinda wasu majiyoyi ke bayyana cewa wandada suka rasa rayukan su zasu kai 70.

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin kasar Burkina Faso za ta dau matakan da suka dace domin zakulo masu hannu a wannan kazamin hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.