Isa ga babban shafi
Kenya

Harin Al Shebaab a Kenya ya hallaka tarin jama'a

Rahotanni daga kasar Kenya sun ce akalla mutane 5 aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wani kazamin hari da wasu Yan bindiga suka kai wani otel da shagunan kasuwanci a birnin Nairobi dai dai lokacin da wasu ganau ke cewa wadanda suka mutun sun tsamma 15.

Tuni dai kungiyar Al Shebaab ta dauki alhakin kai harin wanda ya hada kunar bakin wake da kuma harbe-harbe da bindiga.
Tuni dai kungiyar Al Shebaab ta dauki alhakin kai harin wanda ya hada kunar bakin wake da kuma harbe-harbe da bindiga. Photo: Kabir Dhanji/AFP
Talla

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ya ga gawarwakin da idonsa, yayin da ake musayar wuta tsakanin yan bindigar da jami’an tsaro.

Sai dai wani babban jami'in tsaro da ya tsira da ransa yayin faruwar lamarin ya ce ya ga gawarwaki fiye da 14 a cikin Hotel din kuma ba lallai ya kasance su kadai ba ne.

Tuni dai kungiyar Al Shebaab ta dauki alhakin kai harin wanda ya hada kunar bakin wake da kuma harbe-harbe da bindiga.

Ita ma dai rundunar 'yan sandan kasar ta tabbatar da harin sai dai ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ba.

Yayin musayar wutar tsakanin Jami'an tsaron da mayakan na Al shebaab, jami'an sun yi nasarar tseratar da tarin fararen hular da ga dakunan Otel din da mayakan suka tara su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.