Kotun Kolin Congo za ta fara sauraron karar zabe
Kotun Kolin Jamhuriyar Dimokirdaiyar Congo ta ce, a ranar Talata za ta fara sauraron karar da dan takarar shugaban kasa Martin Fayulu ya gabatar domin kalubalnatar sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana, in da aka bayyana Felix Tshisekedi matsayin wanda ya samu nasara.
Wallafawa ranar:
Sakataren yada labaran kotun, Baudouin Mwehi ya ce, da misalin karfe 9.30 na safe agogon kasar ne, kotun za ta fara zaman sauraron karar.
Hukumar zabe ta bayyana Tshisekedi a mtsayin wanda ya yi na daya, sai Fayulu a matsayi na biyu, yayin da Emmanuel Ramazani Shadary, dan takarar Jam’iyya mai mulki ya zo na uku.
Kungiyar kasashen da ke kudancin Afrikka sun bukaci sake kidaya kuri’un da kuma kafa gwamnatin hadin kai domin samar da zaman lafiya a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu