rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Italiya Bakin-haure Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar da Italiya sun sha alwashin fadada yaki da kwararar baki Turai

media
Firaministan Italiya Giuseppe Conte. REUTERS/Remo Casilli

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da Firaministan Italiya Giuseppe Conte sun sanar da samun gagarumin ci gaba a yakin hadin gwiwar da su ke da kwararar bakin haure ba bisa ka’ida ba zuwa nahiyar Turai ta Jamhuriyyar Nijar.


A cewar Firaminista Giuseppe Conte an samu raguwar kwararar bakin hauren tun bayan kaddamar da shirin hadakar tsakanin Italiya da Nijar a shekarar 2016, ya na mai cewa shekarar 2018 ta zamo mafi karancin kwararowar bakin haure zuwa kasar ta Italiya.

Mr Conte ya kuma yaba da kokarin takwaran na sa na Nijar a fafutukar da ya yi wajen yaki da safarar mutane zuwa Turai.

A cewarsa an samu raguwar ‘yan ciranin da akalla kashi 80 cikin 100 matakin da ya bayyana a matsayin gagarumin ci gaba a yakin da su ke da kwararar baki zuwa Turai.

Shugabannin biyu sun kuma sha alwashin ci gaba da yakin don dakile bakaken fatar da ke tsallaka Turai da nufin samun rayuwa mai inganci, inda Conte ya bukaci kasashen na Turai su kara yawan ayyukan tallafawa rayuwar Afrikawa don hana su kaura.