Isa ga babban shafi
Sudan-Zanga-Zanga

'Yan sanda sun tarwatsa sabbin masu zanga-zanga a Khartoum

Jami’an tsaro sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Khartoum babban birnin Sudan ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa. Tun a Yammacin jiya Talata ne sabuwar zanga-zangar ta barke kasa da sa’o’i 24 bayan jawaban shugaba Omar Al- Bashir don kwantar da hankula.

Yanzu haka dai zanga-zangar ta tasamma wata guda an yi yayinda shugaban kasar ya ce boren ba zai iya hambarar da shi daga kan mulki ba.
Yanzu haka dai zanga-zangar ta tasamma wata guda an yi yayinda shugaban kasar ya ce boren ba zai iya hambarar da shi daga kan mulki ba. AFP
Talla

Daruruwan masu zanga-zangar wadanda suka kunshi mata da maza har ma da kananan yara sun yi cincirundo a yankin El-Kalakla na Khartoum inda su ke daga wasu kwalaye like da rubutu da ke nuna cewa suna bukatar ‘yanci zaman lafiya da kuma adalci.

Sai dai sa’o’i kalilan bayan taruwarsu a yankin gwamnati ta aike da wasu jami’an ‘yan sanda kwantar da tarzoma wadanda suka tarwatsa taron ta hanyar har ba musu barkonon tsohuwa.

Zanga-zangar ta adawa da tsadar rayuwa wadda ta juye zuwa ta kyamar gwamnati da aka faro tun ranar 19 ga watan Disamban bara, yanzu haka ta tasamma wata guda ana yi.

Cikin jawabansa na jiya dangane da masu zanga-zanga Albashir kai tsaye ya dora laifin rurawa da kuma tunzura masu zanga-zangar kan bangarorin adawa inda ya ce zanga-zanga bata isa ta tumbuke shi daga mulki ba, yana mai cewa kamata ya yi su jira shekarar 2020 don gudanar da babban zabe, zaben da Albashir da kansa zai tsaya takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.