rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Al Shebaab

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kawo karshen harin Al shebab a Nairobi

media
Dakarun Kenya a lokacin da suke kokarin murkushe yan kungiyar Al Shebab a Nairobi REUTERS/Baz Ratner

Rahotanni daga kasar Kenya sun ce akalla mutane 15 aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wani kazamin hari da wasu yan bindiga da ake zaton yan kungiyar Al Shebab suka kai wani otel da shagunan kasuwanci a birnin Nairobi.


Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa yace yaga gawarwakin da kan sa, yayin da ake musayar wuta tsakanin yan bindigar da jami’an tsaro.

Tuni kungiyar Al Shebaab ta dauki alhakin kai harin.

Shugaban kasar Uhuru Kenyatta a safiyar yau laraba ya tabbatar da nasarar jami’an tsaro wajen murkushe maharan.

Sufeto Janar na Yan Sandan Kenya Joseph Boinnet yayi bayani kan harin kamar haka.