Dole a kawo karshen cin zarafin masu zanga-zanga a Zimbabwe- MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Zimbabwe ta kawo karshen, yadda jami’an tsaron kasar ke amfani da karfi fiye da kima kan fararen hular da ke tarzomar adawa da matakin kara farashin man fetur da kashi 150 cikin dari.
Wallafawa ranar:
Kididdigar gwamnati ta nuna cewa, mutane uku kawai suka rasa rayukansu a tarzomar, sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce adadin ya zarta haka sosai.
Majalisar ta yi zargin cewa jami’an tsaron kasar na cin zarafin dan adam hadi da kama daruruwan mutane ba bisa ka’ida.
Kiran na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne bayan da a yau Juma’a, Gwamnatin Zimbabwe ta bada umarnin katse layukan Intanet a ilahirin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu