Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Fayulu ya bukaci al'ummar Congo su bijirewa nasarar Tshisekedi

Dan takarar shugabancin Jamhuriyar Congo da ya zo na biyu a zaben kasar Martin Fayulu, ya yi shelar nada kansa a matsayin sabon shugaba, jim kadana bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke, na tabbatarwa da Felix Tshisekedi nasarar lashe zaben.

Sabon shugaban Jamhuriyar Congo mai jiran gado Felix Tshisekedi.
Sabon shugaban Jamhuriyar Congo mai jiran gado Felix Tshisekedi. REUTERS/Olivia Acland/File Photo
Talla

Jim kadan bayan tabbatar da nasarar tasa shugaba mai jiran gado, Felix Tshisekedi ya bayyana cewa nasarar lashe zaben na baki dayan al'ummar Jamhuriyar Congo ce ba tasa shi kadai ba.

Sabon shugaban mai jiran gado, ya yi alkawarin tabbatar da hadin kan kasar, da kuma gina sabuwar Jamhuriyar Congo marar fama da matsalar rarrabuwar kai da kabilanci.

Sai dai Martin Fayulu da ke ikirarin shi ne ya lashe zaben shugabancin na Jamhuriyar Congo da yawan kuri’u sama da kashi 60, yayi watsi da hukuncin da kotun, tare da zarginta da zama yar amshin shatar gwamnatin Joseph Kabila.

Fayulu ya kuma yi zargin cewa an cimma wata yarjejeniyar sirri, tsakanin Tshisekedi mai jiran gado da shugaba Joseph Kabila, domin murde sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.