Isa ga babban shafi
Somalia

Sojin Amurka sun hallaka mayakan al-Shabaab 52

Rundunar sojin Amurka mai lura da nahiyar Afrika, ta ce dakarunta sun yi nasarar hallaka mayakan al Shebaab 52 a yankin Juba da ke Somalia.

Hoton daya daga cikin jiragen yakin Amurka, yayin luguden wuta kan mayakan al Shabaab a Somalia.
Hoton daya daga cikin jiragen yakin Amurka, yayin luguden wuta kan mayakan al Shabaab a Somalia. World Defence Forum/Facebook
Talla

Sojin na Amurka sun ce farmakin jiragen yakin na jiya Asabar, martani ne kan harin da wasu mayakan al Shebaab masu yawa suka kai, kan sansanin sojin Somalia da ke yankin Jilib dake nisan kilomita 370, kudu maso yammacin birnin Mogadishu.

Rundunar sojin na Amurka, ta kara da cewa babu wani farar hula da farmakin jiragen yakin nata ya shafa.

Hallaka mayakan na al Shebaab ya zo ne kwanaki hudu, bayan da kungiyar, ta dauki alhakin, kai hari kan wani Otal a birnin Nairobi na Kenya, inda ta hallaka akalla mutane 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.