Isa ga babban shafi
Sudan-Zanga-Zanga

Sudan: Likitoci sun yi zaman dirshan a Asibitoci kan kisan mambansu

Akalla likitoci 150 ne suka yi zaman Dirshan jiya Litinin a babban asibitin birnin Khartoum na kasar Sudan don nuna alhinin kisan mambansu guda da ke cikin masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Omar Albashir.

Tuni Shugaba Albashir ya musanta yana mai cewa harsashin da aka hallaka likitan ban a jami’an tsaron kasar ba ne.
Tuni Shugaba Albashir ya musanta yana mai cewa harsashin da aka hallaka likitan ban a jami’an tsaron kasar ba ne. Reuters
Talla

Tun a karshen makon da ya gabata ne kungiyar likitocin Sudan ta tsunduma yajin aiki bayan kisan mambanta a zanga-zangar da ta gudana Alhamis din makon jiya yayin wata arangama tsakanin jami’an tsaro da dandazon masu zanga-zangar.

Rahotanni na nuni da cewa likitocin sanye da fararen kaya rike da kwalaye dake dauke da rubutun cewa kisan likita tamkar kisan kasa ne baki daya sun yi zaman dirshan a ilahirin manyan asibitocin birnin inda suka hana duk wani aikin kula da lafiya.

Fiye da wata guda kenan ana zanga-zanga a sassan kasar ta Sudan don neman lallai shugaba Omar Albashir ya sauka daga mulkin da ya shafe kusan shekaru 30 yana yiwa kasar ta Sudan.

Tuni dai kungiyar Amnesty International wadda kafin yanzu ta ce adadin mutanen da jami’an tsrao suka hallaka a zanga-zangar sun haura 40 ta yi ikirarin cewa matakin wani shiri ne na fara kisan mutane mafiya amfani a cikin al’umma shi ne jami’an na Sudan suka fara da kisan likita.

Sai dai Tuni Shugaba Albashir ya musanta yana mai cewa harsashin da aka hallaka likitan ban a jami’an tsaron kasar ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.