rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Kolin Najeriya ta gamsu da shirye-shiryen INEC kan zaben 2019

media
Farfesa Mahmud Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya INEC tare da wasu jami'an hukumar. Ventures Africa

Majalisar kolin Najeriya ta bayyana gamsuwa da yadda Hukumar zaben kasar ke shirin zabe mai zuwa da zai gudana a fadin kasar.


Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana haka bayan shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya yi musu bayani kan halin da ake ciki dangane da shirin gudanar da zaben.

Akeredolu yace Farfesa Mahmud ya ce tuni suka fara horar da ma’aikatan da zasu gudanar da aikin zaben a matakai daban daban, inda majalisar ta bukaci shugaban hukumar da ya yiwa yan Najeriya bayani kan halin da ake ciki.

Gwamnan ya ce Farfesa Mahmud ya tabatar da shirin gudanar da zaben da katin tantance masu kada kuri’a, yayin da ya ce basa fuskantar wata matsala har da na kudaden aiki.