Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

An rantsar da Tshisekedi a matsayin sabon shugaban Congo

An rantsar da Felix Tshisekedi a matsayin zababben shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na ranar 30 ga watan Disamba.

Sabon Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, Felix Tshisekedi yayin karbar rantsuwar kama aiki a birnin Kinshasa. 24/1/2019.
Sabon Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, Felix Tshisekedi yayin karbar rantsuwar kama aiki a birnin Kinshasa. 24/1/2019. REUTERS/OLIVIA ACLAND
Talla

Shugabannin kasashe 17 aka gayyata domin halartar wannan biki da ke gudana a birnin Kinshasa, yayin da kungiyar Tarayyar Turai ta aike da jakada domin ya wakilce ta a bikin rantsuwar.

Sabon shugaban na Jamhuriyar Congo, wanda cikakken sunansa shi ne Felix Tshikesikedi Tshilambo, mai shekaru 55, da kuma ‘ya’ya 5.

Wannan dai shi ne karo na farko da farar hula zai mika mulki cikin ruwan sanyi ga farar hula, tun bayan samun ‘yancin kan Jamhuriyar Congo daga Belgium a shekara ta 1960.

Sakamakon zaben shugabancin kasar ya nuna Felix Tshekedi na da yawan kuri’u kashi 38, yayinda mai bi masa Martin Fayulu ke da yawan kuriu kashi 34.

Ana kallon Felix Tshikesikedi a matsayin wanda ya gaji mahaifinsa dadadden madugun ‘yan adawa a kasar ta jamhuriyar Congo, wato Etinene Tshisekedi da ya kirkiro jamiyar UDPS a shekara ta 1982, wanda Gwamnatin shugaba Mobutu Sese Seko ke matukar shakkarsa.

Mahaifin nasa ya mutu a shekara ta 2017 bayan da ya yi gwagwarmaya da gwamnatocin shugaba Laurent da kuma na Joseph Kabila.

Felix Tshisekedi ya taba cin zaben zama wakili a majalisar Jamhuriyar ta Congo a shekarar 2011, amma yaki zama a majalisar saboda zargin babu adalci, har sai da aka soke kujerar tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.