rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabuwar zanga-zangar yan adawa a Togo

media
Zanga-zangar Togo MATTEO FRASCHINI KOFFI / AFP

A Togo gungun jam’iyoyin adawa sun gudanar da zanga-zanga a jiya asabar a babban birnin kasar Lome a wani yukunrin su na bayyana rashin amincewarsu da zaben yan majalisu kasar ,zaben da jam’iyya mai mulki ta samu kujeru 59 daga cikin kujeru 91 na Majalisar kasar.


Yan adawa da suka samar da wani gungun jam’iyyoyin 14 da aka sani da C14 sun kauracewa zaben da aka yi a wancan lokaci, yayinda wakilan kungiyar Afrika da na kasashen yammacin Afrika na Ecowas suka yaba da yada aka tafiyar da zaben yan majalisu.

Wannan dai ne karo na farko da yan adawa suka shirya zanga-zanga tun bayan zaben yan majalisu, yayinda shugaban kasar Faure Gnassingbe ya sake nada Selom Komi Klassou a mukamin Firaministan kasar ,wanda ba tareda an fuskanci jinkiri ba ya nada majalisar ministocin sa.