Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Macron ya bukaci Masar ta mutunta 'yancin fadar albarkacin baki

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara ziyarar aiki a Masar inda ya ke ganawa da shugaba Abdel Fattah al-Sisi, a ziyarar da ake kyautata zaton batutuwa masu alaka da kasuwanci kare hakkin bil’adama da kuma dankon alakar kasashen biyu su mamaye tattaunawar shugabannin biyu.

Shugaban Faransa Emmnuel Macron tare da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi a birnin alqahira na Masar yayin ziyarar aiki ta kwanaki 3 da Macron ya fara.
Shugaban Faransa Emmnuel Macron tare da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi a birnin alqahira na Masar yayin ziyarar aiki ta kwanaki 3 da Macron ya fara. Ludovic MARIN / AFP
Talla

Emmanuel Macron wanda yanzu haka ya fara ziyarar ta kwanaki 3 a Masar, yayin ganawarsa da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi a safiyar yau Litinin ya bukaci daukar matakan kare hakkin bil’adama tare da bayar da ‘yan cin fadar albarkacin baki a ilahirin sassan kasar.

A wani taron manema labarai da shugabannin biyu suka gudanar wanda ya samu halartar kungiyoyin kare hakkin bil’adama, Macron ya ce akwai bukatar tabbatar da doka a al’amuran da suka shafi kare hakkin bil’adama da kuma tabbatar da zaman lafiya.

A cewar Macron ba hakki ne da ya rataya kan sa ya yi wa al-Sisi huduba kan muhimmancin tsaro da zaman lafiya da kuma kare hakkin bil’adama ba, sai dai batu ne da ya kamata a matsayin Masar na dadaddiyar abokiyar huldar Faransa.

Ka zalika shugabannin a wata kebantacciyar ganawa za su tattauna batun kasuwancin da ya kullu tsakaninsu musamman a cinikayyar makamai dai dai lokacin da Sisi ya sayi jiragen yaki da jiragen ruwa na yaki da kuma tauraron dan adam na tsaro daga hannun Faransar wadanda kudinsu ya haura yuro biliyan guda.

Cinikayyar dai wani bangare ne na yarjejeniyar cinikin makamai da aka kulla tsakanin Faransar da Masar a shekarar 2015 da darajar kudinta ya haura yuro biliyan 5 da miliyan dari biyu.

Akwai dai zarge-zarge da ke nuna cewa da makaman da Faransar ta sayarwa Masar ne, kasar ke amfani da su wajen keta hakkin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.